ABNA24 : An raba wannan taimako ne ga ‘yan gudun hijira a cikin karamar hukumar Faskari da ke cikin jihar ta Katsina, wadanda suka bar gidajensu sakamakon ayyukan ‘yan bindiga da sauran matsaloli na tsaro da ake fama da su a cikin yankunan nasu.
Malam Rabi’u Abdullahi Funtua ne ya jagoranci raba wannan taimako ga ‘yan gudun hijirar, wanda ya hada da magunguna da kuma bargunan lulluba.
Inda ya bayyana cewa, ya mika taimakon ne a madadin jagoran Harkar Musulunci Sheikh Ibrahim Zakzaky, yana mai kara ba su hakuri dangane da irin mawuyacin halin da suka samu kansu a ciki saboda rashin tsaro.
342/